FA'IDAR BOYUWA-3
 Shiryar Da Badini
Jagora shi ne hujjar Allah kuma shiryar da mutane shi ne aikinsa, sannan duk kokarinsa shi ne ya shiryar da mutane domin su samu wannan shiriya din, kuma wani lokaci yana alaka da mutane a fili domin isar da lamarin Allah kuma yana nuna musu hanyar rabauta ta Duniya da lahira, wani lokaci kuma yana amfani da karfinsa domin ya sanya wa mutane tasiri ta hanyar badini kuma yana karkatar da su zuwa ga alheri ta irin wannan hanya wacce take ita ce hanyar kamala da shiriya. A wannan bangare babu wata bukata ga shiriya ta zahiri abin da ake so shi ne shiriya ta badini. Imam Ali ya yi bayanin wannan da cewa:
Ya Ubangiji! ba don akwai hujjarka a Duniya ba wanda zai kama hannun halittu zuwa ga shiriya…, idan da koda ba mu ga wannan samuwa ta Imami a zahiri ba amma babu kokwanto muna ganin koyarwa da tarbiyyarsa a zukatan muminai kuma su suna aiki ne bisa wannan asasin. Imami boyayye yana aiki domin shiryar da mutane domin motsawa da kuma samar da sauki karkashin tarbiyyantarwarsa ta musamman domin su shirya wa zama cikin tawagar wannan Imami, kuma wannan duk yana faruwa ne don albarkar samuwar Imami boyayye.

Kariya Daga Bala'o'i
Babu wani kokwanto cewa kariya da aminci su ne asasin rayuwa, kuma faruwan bala'o'i suna sanya rayuwa ta fada cikin hadarin karewa kuma sarrafa wadanan musibu da kawar da su duk da abubuwan na zahiri suna iya tasir wajen ahaka mama abubuwan badini su suka fi taka rawa a ciki, kuma akwai ruwayoyi na magabata masu yawa da suka zo game da samuwar Imami wanda yake shi ne aminci ga mutanen Duniya gaba daya.
Imam Mahadi (a.s) yana cewa: Ni ne aminci ga mutanen kasa…
Samuwar Imami yana hana saukar musifu ko jawo azabar Allah da fushinsa da sukan iya sauka sakamakon ayyukan fasadi da barna da mutane suke yi. Kur'ani mai girma yana fada cewa: "Allah ba zai azabtar da su alhalin kana cikinsu". Imam Mahadi (a.s) shi ne asasin bayyanar rahamar Allah kuma da shi ne ake kare al'umma daga bala'o'i manya musamman ga al'ummar da take shi'arsa, duk da cewa su kansu Shi'a ba kasafai sukan kula da wannan karamomi nasu ba, ko su fahimci cewa wani hannun boye ne ya taimaka musu.
Imam Mahadi (a.s) yana cewa: Ni ne cikamakon wasiyyai, kuma da ni ne Allah yake kare bala'i daga ma'abotana da Shi'ata.
Zamu iya gani a kwanakin juyin musulunci da kuma yakin daular musulunci ta Iran sauadyawa mabiya Imam Mahadi suka tsallake wani babban tarkon da makiya suke danawa kuma suka karya hukuncin nan na dokar hana yawon dare a 21 ga watan Bahaman 1357, da umarnin Imam Khomaini, kuma duba fadowar helikwaftan Amurka a saharar Dabs a 1359 H.Sh. da kuma gano juyin nan na 21 ga watan Tir 1361, da kuma kasawar makiya a yakin shekaru takwas na yaki.

Ruwan Rahama
Imam Mahadi (a.s) shi ne wanda aka yi alkawari ga Duniya kuma alkibalar burin dukkan muslmi kuma abin so gun Shi'a kodayaushe yana kula da halayen mutane ne, kuma boyuwar wannan ranar rahama da tausayi ba ya hana ta bayar da rayuwa da karfafa masoyanta ta bayan gajimare, kuma ba ya hana ta yi walimar garar baki ga masoyanta. Wannan wata ne shi mai soyayya da kauna mai dauke bakin cikin masu neman taimamkonsa dagamasoyansa, kuma shi ne mai warkar da ciwon masu miki da suka kwanta a gadajen asibiti da suka rasa magani, kuma wani lokaci yakan nuna wa wadanda suka bace hanya a daji. Shi ne mai lallashin zukatan masu sauraronsa, kuma mai ruwan rahamar Allah ga masoyansa. Duba ka ga abin da yake roka wa masoyansa wajen Allah madaukaki da fadinsa: ya kai wanda yake shi ne hasken haske, ya mai juya al'amura ya mai tayar da kaburbura, ka yi tsira da aminci ga Muhammad da alayen Muhammad ka sanya mini mafita ni da shi'ata daga wannan kunci, kuma da farin ciki daga bakin ciki, ka yalwata mana tafarki, ka kuma saukar mana abin da zai faranta mana, ka kuma yi mana abin da kake ahlinsa ne kai, ya mai baiwa.
Wadannan abubuwa da aka kawo suna nuna samuwar Imami a fakuwa da boyuwa, kuma wadanda suke samun haduwa da shi su ne wadanda suke da cancanta da samun dacewa ga hakan.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation