AL-BADA'U -SAMUN CANJIN RA'AYI-
 

Wallafar: Al-Majma'ul alami Li Ahlil-bait
Fassarar: Hafiz Muhammad Sa’id

Kura'ni Da Hadisi Suna Cewa:
“Allah yana shafe abin da yake so, kuma yana tabbatarwa, kuma a gunsa akwai Ummul Kitabi” Surar Ra’adi: 39
“Wanda ya raya cewa, Allah madaukakin sarki yana samun canaji a wani abu, da bai san shi ba jiya, to ka barranta da shi” Biharul Anwar: 4\111, H 30.

Gabatarwar Al-Majma'ul alami Li Ahlil-bait
Lallai yana daga cikin dabi’ar mutane su yi sabani a junansu, sai dai Allah yana son wannan sabanin ya takaita a cikin kewayen ingantaccen imani, saboda haka ne ba makawa ya zamanto akwai ma’auni tabbatacce da masu sabani zasu koma zuwa gare shi. Allah madaukakin sarki ya saukar da littafi da gaskiya domin ya yi hukunci tsakanin mutane da gaskiya cikin abin da suka saba a cikinsa[1].
Da babu wannan gaskiya guda daya, to da al’amarin rayuwa ba zai daidaitu ba, Wannan shi ne abin da Kur’ani yake tabbatar da shi kuma yake bisa ka’idar tauhidi, sannan sai daga baya aka samu karkata da sabani da camfe-camfe har mutane suka nisanta daga wannan asasi nisanta mai girma.
Ta haka ne ta bayyana cewa mutane ba su ne masu cancantar su yi hukunci da gaskiya ko karya ba matukar sun kasance suna iya biye wa son rai da bata da zalunci.
Duk da littafin Allah ya sauka da shiriya ya kuma isa zuwa ga mutane…. tare da hakan son rai ya rinjayi mutane nan da can, kwadayi da tsoro da bata suka nisantar da mutane ga karbar hukuncin littafi da komawa zuwa ga gaskiya da yake dawo da su zuwa gareta.
Bata shi ne ya jagoranci mutane a tsawon zamani zuwa ga sabani da shisshigi da kin Allah, Jahilci ya zama wani sababin sabani da rarraba, sai dai shi jahili ya kamata ne ya tambayi malamai kamar yadda Allah ya fada: “Ku tambayi ma’abota sani idan ba ku sani ba[2]”.
Ta haka ne ketare iyakar jahili ya kasance zalunci da shisshigi ga wannan asali wanda hankali yake amincewa da shi, kuma ma’abota hankula suke karkata zuwa gareshi, kuma lallai wannan shi ne mafi bayyanar ka’idoji da hanyoyi wadanda zasu toshe hanyar rarraba da sabani.
Musulunci shi ne addinin Allah dawwamamme da hakikarsa ta bayyana cikin nassin littafin Allah (S.W.T) da sunnar manzonsa (S.A.W) da ba ya magana da son rai sai da wahayi. Kuma Allah da manzonsa sun sani cewa al’ummarsa zata yi sabani bayansa kamar yadda ta yi sabani a lokacin rayuwarsa, don haka ne Kur’ani mai girma ya sanya wa al’umma makoma da zasu dogara da ita bayan wafatin manzo (S.A.W) tana tafiya tare da shi taku-taku tana kuma gabatar wa al’umma abin da suka takaita ga fahimtarsa da tafsirinsa, wannan kuwa su ne; Ahlul Baiti (A.S), sun tsarkaka ne daga dukkan dauda da kuma kazanta wadanda Kur’ani ya sauka ga kakansu Mustapha (S.A.W), suna karbarsa suna karanta shi suna hankaltarsa da kiyayewa, sai Allah ya ba su abin da bai ba waninsu ba... Kamar yadda manzo ya yi wasiyya da su a matsayin makoma ta gaba daya a hadisin sakalain mash’huri, sai suka kwadaitu wajan kare shari’ar musulunci da Kur’ani mai girma daga fahimta ta kuskure da tafsiri na barna, suka saba da bayanin ma’anarsa madaukakiya, sai suka zama makoma kuma madogara ga al’ummar musulmi, suna kore shubuha suna masu karbar tambayoyi da hakuri da juriya. Bayan nan abin da suka bari mai yawa yana shaidawa da kyawon mu’amalarsu tare da masu tambayarsu da tattaunawa da su, kuma komawa garesu da zurfin amsawarsu yana nuni zuwa ga kasancewarsu makoma ta ilimi a wannan fage.
Hakika koyarwarsu ta kare abin da suka bari, kuma mabiyansu suka kwadaitu a kan kare shi daga tozarta, abin da yake nuni zuwa ga koyarwarsu da ta tattaro dukkan wasu rassa na ilimomin da suke kunshe cikin koyarwar addinin musulunci.
Kuma wannan makaranta ta iya tarbiyyatar da mutane da suke shirye domin kamfata daga wannan ilmi kuma ta fitar wa al’umma manyan malamai masu biyayya ga tafarkin Ahlul baiti (A.S), suna masu gamewa da sanin dukkan mas’alolin mazhabobi daban-daban, da kuma akidoji a cikin da’irar musulunci da wajanta, suna masu bayar da mafi kyawon amsa da bayanai a tsawon zamanin da ya gabata.
Hakika majma Ahlul baiti (A.S) ya gaggauta yana mai farawa daga nauyin da yake kansa da ya dauka a kafadunsa domin kariya ga sakon musulunci wanda ma’abota mazhabobi da kuma masu akidu da suka saba wa musulunci suka damfaru da su, yana mai bin tafarkin Ahlul Baiti (A.S) da mabiyansu da suka kwadaitar da raddi kan kalu-balen wannan zamani da kuma kokarin dawwama a kan tafarkin gwagwarmaya daidai gwargwadon abin da kowane zamani yake bukata.
Ilimin da littattafan malamai masana ma’abota bin koyarwar Ahlul baiti (A.S) suka taskace shi a wannan al’amari ba shi da misali, domin shi madogara ce ta ilmi da yake karfafa da dogara da hankali da hujja, yake kuma nisantar son rai da zargi, yake kuma magana da malamai masu tunani daga ma’abota kwarewa, maganar da hankali yake yarda da ita kuma dabi’ar dan Adam kubutacciya take karbar ta.
Kokarin majma ya zo ne domin ganin an gabatar wa dalibai sabuwar marhalar wannan ilimi mai wadata a shafin tattaunawa da tambaya da kuma raddin shubuha da a kan tayar daga lokaci zuwa lokaci tsawon zamani, ko kuma ake kawo wa a yau musamman ma da taimakon wasu kungiyoyi masu kin musulunci da musulmi a cikin sarkar sama ta intanet da makamantansu, muna masu nisantar abin da yake maras kyau, muna masu kwadayin motsa tunanin masu hankali da masu neman gaskiya domin su bude idanunsu a kan gaskiyar da koyarwar da Ahlul baiti (A.S) suka gabatar wa duniya baki daya a zamanin da hankula suke cika, alakar mutane da tunani take samuwa cikin gaggawa.
Ba makawa mu yi nuni da cewa wannan tattararrun bahasosi an tanade su ne a lujna ta musamman da Hujjatul Islam Abul Fadal Islami yake shugabanta tare da wasu manya da suka hada da Sayyid Munzir Hakim, da Shaikh Abudlkarim Bahabahani, da Sayyid Abdurrahim Musawi, da Shaikh Abdul Amir Assuldani, da Shaikh Muhammadul Amini, da Shaikh Muhammad Hashimi Al’amili, da Sayyid Muhammad Rida aali Ayyub, da Shaikh Ali Baharami, da Husaini Salihi, da Aziz Al’ukabi.
Kuma muna mika godiya mai yawa ga dukkan wadanan da kuma ma’abota falala da bincike da suka hada da: Shaikh Yusuf Garawi, da Shaikh Ja’afarul Hadi, da Ustaz Sa’ib Abdulhamid, domin bibiyar da kowannensu ya yi wa wadannan bahasosi da kuma bayanansu masu kima.
Fatanmu shi ne ya zama mun gabatar da abin da zamu iya na kokarin sauke nauyin da yake kanmu game da wannan sako mai girma na ubangijinmu da ya aiko manzonsa da shiriya da kuma addinin gaskiya domin ya daukaka shi a kan dukkan wani addini kuma Allah ya isa shaida.
Al-Majma'ul alami Li Ahlil-bait
Birnin Kum – Iran
Bada'u A Cikin Kur’ani Mai Girma
Ana la’akari da Bada’ a cikin al’amura na kalam na tauhidi da aka tayar da bahasi mai fadi a kansa tsakanin malaman Ilimin Sanin Allah. Wannan kuma ya faru saboda wasu abubuwa masu jan hankali da suke kan maganar Bada ne. Domin Bada a lugga yana nufin bayyana bayan boyuwa. yana kuma hadawa da tattaunawa ta al’ada, da kuma wajan musanya ra’ayoyi da tunani da hadafi da manufofi, misalin a kan ce: “Da ra’ayinsa kaza ne sannan sai ya samu canji a game da ra’ayin” Abu ne sananne cewa canjin ra’ayi da wannan ma’ana tana kunshe da ma’anar jahilci da ya rigaya, da kuma faruwar sabon ilmi kan al’amarin. kuma dukkansu koraru ne ga Allah madaukakin sarki domin ilmin Allah madaukakin sarki ainihin Allah ne, babu wani jahilci da ya rigaye shi.
Sai dai idan muka zurfafa tunani kan ma’anar Bada a ma’anarsa ta lugga to zamu same shi yana hauhawa daga abu biyu ne:
1-Jahilci da ya rigaya.
2-Canjin ra’ayi da manufa da hadafi sakamakon sabon ilimin da aka samu.
Sai mu tambaya wanne ne daga wadannan al’amura guda biyu yake kore Tauhidi? Na farko ko na biyu?
Kuma shin zai yiwu a raba tsakaninsu? Ta yadda za a samu wani canji a ra’ayi ba tare da ya kasance daga jahilci da ya rigaya ba ko kuma ilimi sabo da ya faru ba?
Amma tambayar farko: Zamu ga cewa a sarari yake cewa al’amari na farko yana kore tauhidi, kuma babu wani musulmi da ya karbi jingina wa Allah madaukakin sarki jahilici.
Amma abu na biyu: Idan canji ya zama yana lizimtar zati domin jahilci da ya gabata ne da kuma samuwar ilimi da ya zo. to a nan yana kore tauhidi, kamar yadda jahilci yake kore tauhidi haka ma canji yake kore shi. Amma idan canji ba ya samun zati yana faruwa daga wani abu daban to anan ba ya kore Tauhidi.
Wanna canjin na ra’ayi da yake lizimtar zati domin bayyanar ilimi da kuma bacewar jahilci, saboda haka ne kamar yadda ba zai yiwu a jingina jahilci ga Allah ba haka nan ba zai yiwu a jingina masa canji a ra’ayi ba (S.W.T) domin wannan yana nuna ilimi ne da aka samu, alhalin ilimin Allah ba wanda ake nema ba ne domin a samu. Shi iliminsa na zatinsa ne wanda yake shi mai tsayuwa ne da samuwar zatinsa.
Da wannan ne jawabin wadanna tambayoyi biyu ya bayyan a fili, kuma bari mu gani shin akwai aya a kur’ani da ta dangantawa Allah canji a wani al’amari, ko wani bangare?
Akwai wadanda sukan amsa cikin gaggawa game da wannan suna masu cewa alkur’ani mai girma ya kore duk wani canji ga Allah (S.W.T) suna masu dabbaka wannan aya: “Ba zaka taba samun juyi ba ga sunnar Allah”[3]. “Ba zaka taba samun canji ba ga sunnar Allah”[4].
Sai dai wanan jawabi bai isa ba, domin kur’ani wani abu ne da ake fahimtarsa daga dukkan kur’ani, ba daga wani bangare ba kawai. Wannan kusan muna iya cewa yana zama rabin amsa ne, domin akwai wani bangare da yake jingina canji ga Allah da cewa: “Allah yana shafe abin da ya so yana kuma tabbatar da abin da ya so kuma a gunsa akwai Ummul kitab”[5].
Da fadinsa madaukakin sarki: “Allah ba ya canja abin da ke ga mutane har sai sun canja abin da yake ga kawukansu”.
Aya ta farko tana nuna Allah yana shafe abin da ya so yana kuma tababtar da abin da ya so wanda wannan yake nuna canji da sakewa, amma aya ta biyu ta shelanta a fili cewa Allah ba ya canja halin mutane idan suka canja abin da yake ga kawukansu. Al’amarin tattalin arziki da siyasa na mutane yana nufin wani abu ne da Allah yake kaddara shi da zai iya karbar canji idan mutane suka canja rayuwarsu daga shirka zuwa ga imani, daga bata zuwa ga shiriya, to a nan akwai kaddarawa guda biyu; kaddarawa da ta zo daga halin mutane na biyayyarsu, da kuma kaddarawar Allah garesu a halin sabonsu, idan suka zabi biyayya sai a gudanar musu da na farko idan kuma suka zabi sabo sai a gudanar musu da al’amari na biyu, da kana ne abin da ya zo a ruwaya da yake nuna tasirin ayyuka wajan arzutawa da ajali da bala’o’i yake nuni.
Wannan kuma ba wanda ya saba daga muslumi game da hakan; sabani ya samu ne kan ma’anar “Bada” idan aka fassara shi ta yadda zai saba da ma’anar da ya saba da lugga da ya kore tauhidi, amma sabanin zai kau idan aka komawa ma’anar da ake nufi a isdilahi da ba ya lizimtar danganta jahilci ga Allah (S.W.T). Abin da ake nufi a koyarwar Ahlul baiti (A.S) shi ne “Allah yana kaddara wa bayi wani abu sannan sai ya canja sakamakon wani abu sabo da ya bayyana daga bawa sakamakon wani aiki daban da ya yi, tare da cewa Allah ya riga ya san duka al’amuran biyu zasu faru a dukkan halayen biyu”.
Da sun san wannan ma’ana da sun san cewa wannan wani abu ne da dukkan msulmi suka hadu akansa. Shi ya sa jayayya din kan lafazi ne kawai, kuma Allama Sayyid Abdulhusaini Sharafuddin ya yi gaskiya yayin da ya ce: “Jayayya tsakaninmu da Ahlussunna ta lafazi ce. Sannan sai ya ce: Idan waninmu ya dage a kan wanann jayayya ya ki yadda da ma’anar ‘Bada’ kamar yadda muka fada, to mu sai mu sauka a kan hukuncinsa sai ya canja lafazin da abin da ya so, ya kuma ji tsoron Allah a kan dau’uwansa mumini[6].
Kafinsa akwai Shaihul Mufid a littafinsa yana cewa; “Amma amfani da kalmar Bada wannan ruwaya ce ta zo da ita wacce abu ne da yake tsakanin Allah da bayinsa, ba domin ruwaya ta zo da shi ba da take da inganci da bai halatta ba a yi amfani da shi ga Allah (S.W.T), kamar yadda da ba don ruwaya ta zo da cewa Allah yana fushi, yana yarda, yana so, yana jiji-da-kai, da bai halatta a gaya masa haka ba, sai dai yayin da ya zo a ruwaya sai ya zama yana da ma’anar da hankula suka tafi akai da ba sa kin ta, kuma tsakanina da sauran msulmi a wannan babi babu sabani, kawai sabanin da ake dashi a lafazi ne ba a wani abu ba, na kuma riga na yi bayanin dalili na a kan amfani da wannan lafazi. Wannan kuma shi ne mazhabar imamiyya gaba daya, kuma duk wanda ya saba wa wannan mazhaba yana sabani ne a lafazi ba a ma’ana ba[7].
Kafinsa Imam Assadiq (A.S) ya fada a tafsirin ayar nan: “Allah yana shafe abin da ya so yana kuma tabbatar wa kuma a gunsa akwai Ummul kitab”. Ya ce; “Dukkan wani al’amari da Allah yake son shi to akwai shi a cikin iliminsa kafin samar da shi, ba wani abu da yake bayyana gareshi sai ya kasance da ma can yana da ilimi da shi, Allah ba ya canja wa sakamakon jahilici”[8]. A wani hadisin yana cewa: “Wanda ya raya cewa Allah madaukakin sarki yana samun canaji a wani abu, da bai san shi ba jiya, to ka barranta da shi”[9]. Sannan madogarar dalilin imamiyya a mas’alar Bada a bu uku ne:
1-Faidansa: “Allah yana shafe abin da da ya so ya kuma tabbatar da abin da ya so kuma a gunsa akwai Ummul kitab”[10].
Da fadinsa: “Wanda yake sama da kasa yana tambayarsa, kowace rana yana cikin sha’ani ne”[11].
2-Kamantuwar wanann mas’ala da mas’alar shafe hukunci a shari’a, Bada shafewa ne a samarwa, Naskh kuma shafewa ne a hukunci. Kamar yadda msulmi suka tabbatar da shafewa ga hukunci a shari’a kamar a mas’alar alkibla daga masallacin al’akasa zuwa ga masallacin ka’aba, kuma ba wanda ya saba a wannan na daga musulmi. Wannan kuma ba a gan shi a matsayin canji a ilimin Allah ba, bai kuma lizimtawa Allah jahilci ba da ya gabata, haka nan mas’alar Bada canji ne amma a samarwa ba tare da ya lizimta wa Allah jahilci da ya rigaya ba, ko sabawa ga iliminsa na tun fil azal, idan wani ya kawo matsala game da Bada, to sai ya kawo matsala game da shafewa, abin da duk muka fada game da shi a babin shafe hukunci haka ma yana iya zama dalili a babin Bada ba tare da wani bambanci ba ko kadan tsakanin al’amuran biyu. Suka a kan Bada yana zama maimaitawa ne ga sukan da yahudawa suka yi wa shafe hukunci a farkon shari’a yayin da suke ganin wanan bata ne da kuma rashin yiwuwar danganta shi ga Allah (S.W.T) kamar yadda ya zo na daga amsoshi da malaman msulmi suka ba su da kuma tabbatar musu da yiwuwar shafe shari’a ba tare da wanan ya lizimta samuwar tawaya ga zatin Allah madaukakin sarki ba, haka ma wannan yake yiwuwa ga Bada a babin halittawa da samarwa da kuma tafiyar da al’amuran bayi.
3-Tasirin ayyuka a game da makomar mutum; wanan kuma gaskiya ce tabbatacciya ta kur’ani, hada da cewa sunnar annabi mutawatira ta zo da karfafawa a kan hakan, da cewa ayyukan mutum na imani, da shirka, da biyayya, da sabo, da bin iyaye, da saba musu, da ciyar da talakawa, da kamewa ga barin hakan, da sadar da zumunci, da yankewa,… duk suna da tasiri wajan arziki da albarkar da kuma tsawon rayuwa da sa’ada. Wadannan al’amura suna daga abubuwan da kur’ani ya ambata saudayawa, kuma sunnar annabi ta karfafa su.
Fadinsa madaukaki “Allah ba ya canja abin da yake ga mutane har sai sun canja abin da yake garesu”. Wanda yake musun Bada musunsa zai kai shi zuwa ga musun wannan hakika bayyananniya ce koda kuwa yana imani da ita, ya sani cewa wannan abin da yake imani da shi, shi ne imamiyya take kira da Bada.